Isa ga babban shafi
Amurka-India

Kotun Amurka ta yanke hukuncin daurin shekaru 35 ga wanda ya kitsa harin Mumbai

Wata kotun kasar Amurka ta yanke wa David Coleman Headley zaman gidan yari na tsawon shekaru 35, wanda aka kama da laifin taimaka wa tsegerun kasar Pakistan, da suka kai wani mummunan hari a Mumbai a shekarar 2008.

Ma'aikatan agaji a wani wurin da aka kai hari a Mumbai
Ma'aikatan agaji a wani wurin da aka kai hari a Mumbai Reuters
Talla

Headley, Dan shekaru 52 na haihuwa, ya amsa laifinsa har da amsa wani shirin kai hari ga wani Gidan Jarida, wanda hakan ya sa aka mai rangwamen hukunci, daga hukuncin kisa zuwa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 35.

Akalla mutane 166 suka mutu a harin na Mumbai, yayin da wasu daruruwa suka jikkata bayan wasu tsegeru dauke da makamai suka kwashe kwanaki uku suna kai hare-hare a birnin na Mumbai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.