Isa ga babban shafi
India

Dangantaka tsakanin India da Pakistan na dada tabarbarewa akan kisan Soji biyu a yankin Kashmir.

Takaddama ta kaure tsakanin kasashen India da Pakistan, kan kisan da aka yi wa sojojin India biyu a yankin Kashmir, abinda ya dada jefa yankin na kasar ta India cikin rudani.Dama dai kasashen India da Pakistan na fama da matsalolin dangantaka da ta dade tana tsami tsakanin kasashen biyu. 

Jami'an tsaron kasar India na kokarin kwantar da hankalin masu zanga-zanga a yankin Kashmir.
Jami'an tsaron kasar India na kokarin kwantar da hankalin masu zanga-zanga a yankin Kashmir. Reuters/Fayaz Kabli
Talla

A karon farko kasar India ta aike da sammaci ga Jakadan kasar Pakistan dake birnin New Delhi Salman Bashir, dan nuna bacin ranta kan kisan da aka yiwa sojojin ta biyu a Kashmir, abinda ya sa ministan harkokin wajen kasar, Salman Khurshid ya ce zasu mayar da martanin daya dace kan lamarin.

Rahotanni sun ce, anyi kaca kaca da gawar daya daga cikin sojojin na India, abinda ya dada harzuka jami’an kasar.

Sai dai Pakistan ta musanta cewar sojojin ta sun kashe Dakarun biyu, kamar yadda wani baban jami’in Sojin kasar ya shaidawa takwarorin sa na kasar India.

Pakistan tace, labarin wani yunkuri ne na dauke hankalin duniya, ta hanyar farfaganda kan kisan da aka yiwa sojin Pakistan guda ranar lahadi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.