Isa ga babban shafi
India

An kashe wasu 'yan gwagwarmayar yankin Kashemir su biyu

Rahotanni daga kasar India na nuna cewa ‘Yan kasar sun harbe wasu da ake zargin masu tsatsauran kishin Islama ne su biyu a yankin Pulwama da ke Kashmir, kana wasu fararen hula bakwai suka sami raunuka a lokacin da suke boren kashe mutanen biyu da aka yi.

Firaministan kasar India, Manmohan Singh
Firaministan kasar India, Manmohan Singh www.theunrealtimes.com
Talla

A cewar Mataimakin ‘yan sanda Vijay Kumar, mutanen biyun da aka kashe na da hanu a wani harin bam da aka kai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mata hudu ‘Yan yawon bude ido a yankin na Kashmir.

Ya kara da cewa, a yanzu haka an saka dokar hana fita a yankin.

Kasar India dai na zargin kasar Pakistan da marawa masu tsatsauran ra’ayin kishin Islama baya, inda suke kai munanan hare-hare a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.