Isa ga babban shafi
India

Sashin kiwon lafiyar India ya tabarbare gaba daya, inji Minista

Minista mai kula da cigaban karkara a kasar India, Jairam Ramesh ya ce sashin kiwon lafiyar kasar ya tabarbare gaba daya, inda fiye da kashi 70 na kudaden da mazauna karkara ke kashewa akan kiwon lafiya ne, wanda kuma haka yake sakasu cikin kangin basussuka. Ramesh wanda ya yi fice wajen tsage gaskiya, ya jaddada cewa hakan na nuna cewa sashin na kiwon lafiya a kasar baya tabuka komai. 

Firaministan kasar India, Manmohan Singh
Firaministan kasar India, Manmohan Singh www.theunrealtimes.com
Talla

“Duk mun sani cewa sashin kiwon lafiya a India ya tabarbare gaba daya.” Ramesh ya bayyana a wani taro da aka yi a birnin New Delhi.

Ya kara da cewa, yankunan karkara da dama a kasar ta India, babu ababan kiwon lafiya.

Rahotannin sun nuna cewa, mafi akasarin mutanen India daga kowane rukunin jama’a, sun gwammace su ziyarci asibitoci masu zaman kansu a maimakon asibitocin jama’a, wadanda a lokuta da dama ake kuka babu ma’aikata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.