Isa ga babban shafi
India

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a hukunta wadanda suka kashe wata mata ta hanyar fyade a Indiya

Shugabar asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin duniya wato UNICEF Uwargida Michelle Bachelet, ta bukuci hukumomin kasar Indiya da su gudanar da bincike tare da hukunta masu hannu a asikata fyaden da ya yi sanadiyyar mutuwar wata yarinya ‘yar asalin kasar ta Indiya a cikin kwanakin da suka gabata.

Talla

Bachelet wadda tsohuwar shugabar kasar Chili ce, ta bayyana wa manema labarai a birnin Abuja na tarayyar Najeriya inda take gudanar da ziyarar aiki a wannan juma’a cewa, akwai bukatar kasashen duniya cikinsu kuwa har da Indiya su samar da tsauraren dokoki domin hana cutar da mata da ake yi a wannan zamani.

To sai dai shugabar asusun na UNICEF, ta ce duk ya ke akwai dokokin da suka tanadi yadda za a hukunta wadanda aka sama da hannu a aikata irin wannan laifi, to amma ba kasafai ake zartar da dokokin ba a cewarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.