Ana nazarin Na’urar Wasannin Bidiyo na iya sa yara aikata ta’asa
Kisan mutane 26 da suka hada da kananan yara 20, da wani matashin Dan bindiga ya yi, a wata makarantar Newtown a Jihar Connecticut, ya sake takalo muhawarar da aka dade ana yi kan tasirin da Na’urar wasannin Bidiyo da ake kira “Videogames” ke yi ga masu tunanin daukar makamai.
Wallafawa ranar:
Kwararru sun dade suna muhawara kan ko wadannan mahajjojin na kwanfutar da ake kira Videogames, da ke dauke da fina-finan tashin hankali irin su "Assassin's Creed," "Thrill Kill" ko "Manhunt - Executions", sun kasance wata taswirar da ke dora yara zuwa ga aikata ta’asa.
Wasu ‘Yan siyasan Amurka sun bayyana rawar da shirye-shiryen talibijin da Fina-finai da Na’urar wasanni ta Bidiyo ke takawa wajen aikata ta’asa, kuma Gwamnan Jihar Colorado John Hickenlooper, na da irin wannan ra’ayin, tun bayan da aka hallaka wasu mutane 12 a wani gidan kallon da ke kusa da birnin Denver a watan Yuli.
Hickenlooper ya shaidawa kafar yada labaran Telebijin ta CNN cewa, da alama idan wasu mutane masu karamar kwakwalwa suka kalli wasu fina-finan Na’urar Wasanni ta Bidiyo, za su rinka daukar kan su kamar sune a ciki.
Shi ma Sanata Jay Rockefeller ya bayyana lamarin na baya-bayan nan, da cewa wata manuniya ce da ke kiran a dauki kwararan matakai.
Yace ba tabbas kan ko irin wadancan hotunan ne suka yi tasiri ga Dan bindigan Newtown, yana mai cewa muhimmin abu shi ne dole a sa ido kan irin wadannan fina finai na wasannin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu