Isa ga babban shafi
Amurka

An fara binne yaran da Dan bindiga ya kashe a Amurka

An fara binne gawar wasu yara daga cikin wadanda wani matashin dan bindiga ya bindige a wata makaranta da ke a Newtown jahar Connecticut, al’amarin da ke neman gwamnatin Amurka ta kafa dokar haramta mallakar Bindiga.

shugaban Amurka Barack Obama yana kwalla bayan ya kai ziyara makarantar Sandy Hook a Newtown, Connecticut. da wani matashin dan bindiga ya bindige yara 20
shugaban Amurka Barack Obama yana kwalla bayan ya kai ziyara makarantar Sandy Hook a Newtown, Connecticut. da wani matashin dan bindiga ya bindige yara 20 REUTERS/Yuri Gripas
Talla

A ranar Juma’a ne Wani matashin dan bindiga ya bindige yara  20 yawancinsu masu shekaru tsakanin Shida zuwa Bakwai da kuma wasu manyan mutane guda shida bayan bindige mahaifiyar shi.

Gawan kananan yaran biyu, Noah Pozner da Jack Pinto, cikin akwatuna sun kasance na farko da aka binne daga cikin gawawwaki 28 da matashin ya bindige kafin ya kashe kanshi.

Fara binne gawawwakin ya biyo bayan ziyarar da Shugaban Amurka Barack Obama ya kai wa iyayen mamatan.

Har ya zuwa wannan lokaci dai, kamar yadda babban likitan asibitin da aka ajiye gawawwakin mamatan ke cewa, babu wani da ya zo domin karban gawan matashin da ya yi wannan aika-aika mai suna Adam Lanza da gawar mahaifiyar shi daya fara kashewa, mai suna Nancy.

Mahaifin matashin Peter Lanza, bai ce zai dauki dawainiyar dan nasa da tsohuwar matar tasa ba, domin a cewar sa har ya zuwa wannan lokaci yana ta mamakin wannan al’amari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.