Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya lashi takobin hana amfani da bindigogi

Shugaban Amurka, Barack Obama ya lashi takobin amfani da karfin ikonsa wajen hana amfani da bindigogi wajen kisan mutane barkatai, kamar yadda aka yi wa yara kanana 20 a wata makaranta a Jihar Connecticut. Lokacin da yake jawabi ga al’ummar garin Newtown, Shugaban ya ce dole a dakatar da irin wadannan muggan halayen, inda ya ce yana matukar bakin ciki kan kisan da shi ne irin shi na hudu, tun da ya hau karagar mulkin kasar. 

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Jason Reed
Talla

A halin da ake ciki kuma, wata ‘Yar majalisar dokokin kasar daga jama’iyyar Democrat, ta fara neman goyon bayan sauran ‘Yan majalisar, don ganin an haramta rike muggan makamai a kasar.
 

Dianne Feinstein, da ke shugabancin kwamitin leken asirin a Majalisar, ta ce tana da yakinin shugaba Obama zai goya mata baya, a lokacin da za ta gabatar da kudurin dokar a gaban majalisa, ranar 3 ga watan Janairun shekara mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.