Isa ga babban shafi
Amurka

‘Yan sandan Amurka sun tabbatar da mutuwar mutumin da ya kashe yara 20

‘Yan sanda a kasar Amurka sun tabbatar da mutuwar mutumin nan da ya kasha yara kanana 20, da manya 6, a wata makarantar Piramare a jihar Connecticut, da cewa sunan shi Adam Lanza, mai shekaru 20.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Yuri Gripas
Talla

‘Yan sandan sun kuma bayar da tabbacin cewa matashin ya kashe kanshi ne bayan aika-aikar, da ya faro da kashe mahaifiyar shi, mai suna Nancy, a gidan su, bayan da ya yi ta harbin ta.
 

Wani jami’in ‘yan sanda mai suna Paul Vance, ya ce Lanza ya harbi kan shi da wata karamar bindiga, sai dai bai bayyana dalilan da suka sa Lanza ya aikata ta’asar ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.