Isa ga babban shafi
Philippine

Yau Shugaban Philippine zai ziyarci yankunan da guguwa ta yi barna

A yau juma’a, Shugaban kasar Philippine, Benigno Aquino, ya ziyarci yankunan da mahaukaciyar guguwa ta afkawa, inda ya lashi takobin kawo karshen irin wannan bala’in a kasar.

Daya daga cikin yankunan da guguwar ta yi barna a Philippines
Daya daga cikin yankunan da guguwar ta yi barna a Philippines REUTERS/Erik De Castro
Talla

Kusan mutane 500 ne suka rasa rayukansu, sakamakon guguwar mai suna Bopha, da ta afkawa yankunan tsibrin Mindanao, da ke kudancin kasar, a ranar Talata da ta gabata.
 

Wasu daruruwan mutanen sun bata sakamakon guguwar, yayin da mutane fiye da dubu 300 suka rasa gidajensu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.