Isa ga babban shafi
Philippine

Mutane 274 ne suka mutu sakamakon mahaukaciyar guguwar kasar Philippenes

Yawan mutanen da suka mutu, sakamakon guguwa, da ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar Philippines sun karu zuwa 274, a ranar Laraban nan. Rahotannin da ke fitowa daga kasar na nuna cewa, wasu daruruwan mutanen sun bace, a daidai lokacin da masu aikin ceto ke kokarin kaiwa ga yankunan da ambaliyar ruwan da kuma zaftarewar kasa, suka raba su da sassan kasar.A ranar Talata, guguwar da ake wa lakabi da Bopha, ta afka wa tsibirin Mindanao, da ke kudancin kasar, inda ta yi sanadiyyar kayar da itatuwa, da rushe gidaje da daman gaske, kafin ta nufi kasar China.Jami’an gwamnatin kasar, Mar Roxas da Corazon Soliman, da suka ziyarci yankin don gane wa idanun su ta’adin da ambaliyar ta yi, sun bayyana lamarin da cewa mai tayar da hankali ne, yayin da suka ga dubun dubatar gidaje a rushe, tare da gawarwakin mutane a warwatse.Mai Magana da yawun rundunar sojan yankin Laftanar Kanar Paniza, yace 3 daga cikin sojoji masu aikin ceto sun rasa ran su a yankin New Bataan, yayin da 8 suka bace. 

Wasu mutanen da guguwar Bopha ta raba su da gidajen su
Wasu mutanen da guguwar Bopha ta raba su da gidajen su
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.