Isa ga babban shafi
Iran-NAM

Taron kasashen ‘Yan baruwanmu a Iran

Shugabannin kasashen Duniya yawancinsu daga kasashe masu tasowa za su halarci taron kwanaki biyu a birnin Tehran wanda ake sa ran zai kalubalanci manufofin Amurka da sauran manyan kasashen Duniya. Gwamnatin Iran ta shirya taron ne domin kalubalantar kasashen Yammci da ke adawa da shirinta na Nukiliya.

Shugaba Ayatollah Ali Khamenei  da Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad
Shugaba Ayatollah Ali Khamenei da Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad
Talla

Shugaba Ayatollah Ali Khamenei ne zai gabatar da jawabon bude taron a ranar Alhamis inda ake sa ran halartar sabon shugaban kasar Masar Muhammed Mursi da shugabannin kasar India da Pakistan da Lebanon da Sudan da Zimbabwe.

Akwai wakilai kuma da za su halarci taron domin wakiltar shugabannin kasashen Korea ta Kudu da Venuzeula da Syria wadanda dukkaninsu kawayen gwamnatin Iran ne.

Muhimman batutuwan da za su mamaye taron sun hada da la’antar Takunkumin da kasashen Yammaci suka kakabawa kasar Iran da sauran kasashen kungiyar ‘Yan baruwanmu. Taron kuma zai tattauna hanyoyin magance rikicin kasar Syria da aka shafe fiye da shekara ana yi.

Akwai kuma batun samun ‘Yancin Faledinawa, tare da tattatuna ayyukan ta’addanci da kare hakkin Bil’adama.

A shekarar 1961 aka kirkiro kungiyar NAM ta ‘Yan baruwanmu a lokacin yakin Amurka da Daular Soviet. Kuma a yau Kungiyar ta kushi kasashe 120 cikinsu har da Falesdine.

Kungiyar ta kunshi kashi biyu cikin uku na kasashe masu wakilci a Majalisar Dinkin Duniya, wanda haka ne ya sa Ban Ki-moon zai halarci taron duk da Amurka da Isra’ila sun nemi ya kauracewa taron.

Ana sa ran Ban Ki-moon zai gargadi kasar Iran game da shirinta na sarrafa sinadarin Nukiliya da batun kare hakkin Dan Adam.

Wannan ne kuma karon farko da shugaban kasar Masar zai kai ziyara kasar Iran tun a shekarar 1975 da kasashen biyu suka katse huldar Diflomasiya lokacin da Masar ta jagoranci yarjejeniyar zaman Lafiya da Isra’ila.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.