Isa ga babban shafi
Iran-Palestine-Hamas

Shugaban Hamas a Gaza zai kauracewa Taron ‘Yan baruwanmu a Iran

Firaministan Gwamnatin Hamas, Isma’il Haniya a zirin Gaza yankin Falastinawa, yace zai kauracewa taron kasashe ‘Yan baruwanmu, wanda za a gudanar a birnin Tehran na kasar Iran, bayan da shugaban Falastinawa Mahmud Abbas ya yi barazanar kauracewa taron idan za su yi ido da Haniya.

Shugaban Gwamnatin Hamas, Ismail Haniya yana Jaogantar taro tare da Jami'an shi.
Shugaban Gwamnatin Hamas, Ismail Haniya yana Jaogantar taro tare da Jami'an shi. AFP PHOTO/MAHMUD HAMS
Talla

kakakin Firaministan Taher al-Nounou yace, Haniya zai kauracewa taron ne don gudun haifar da rarrabuwar kanu a tsakanin Falastinawa.

Da farko Firaministan ya amince da gayyatar zaman taron da shugaban Iran Mahmud Ahmadenajad ya yi masa a matsayin bako na musamman, amma daga baya ya yi watsi da goron gayyatar.

Tuni dai shugaban Falestinawa Mahmud Abass ya yi barazanar kauracewa zaman taron na Tehran, idan har kasar Jamhuriyar musulunci ta Iran ta gayyaci shugaban gwamnatin Hamas mai ra’ayin Islama a yankin Gaza a taron.

A ranar Lahadi ne Kasar Iran ta bayyana neman goyon bayan kasashe ‘Yan ba ruwanmu dangane da matsayin lambar kasashen yammaci kan shirinta na nukiliya, da kuma tattaunawa rikicin yankin Falastinawa da kuma rikicin kasar Syria,

Taron na kwanaki biyu za’a fara yin sa ne a ranar 30-31 ga Agusta a birnin Tehran babban birnin kasar Iran.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.