Isa ga babban shafi
NATO/OTAN-Afghanistan

NATO zata mika ragamar tsaro ga dakarun Afghanistan a 2013

Shugabannin kungiyar kawancen tsaro ta NATO/OTAN sun kullla wata sabuwar yarjejeniyar hannunta tafiyar da sha’annin tsaro ga dakarun Afghanistan a tsakiyar 2013 bayan kammala taron kwanaki biyu a kasar Amurka.

Taron shugabannin kungiyar Tsaron kwancen NATO
Taron shugabannin kungiyar Tsaron kwancen NATO REUTERS/Eric Feferberg/
Talla

Yarjejeniyar Kungiyar dai ta amince da bukatar Amurka akan kaucewa yin gaggawar ficewa daga Afghanistan kafin shekarar 2014.

Sai dai an kammala Taron kungiyar ba tare da fito da hanyoyin kawo karshen rikicin Taliban ba bayan ficewar NATO.

Matakin kasar Faransa na yunkurin ficewa da dakarunta a watan Disemba shekaru biyu kafin wa’adin NATO, yasa cusa shakku ga wasu kasashen su fara tunanin ficewa.

A lokacin gudanar da taron Daruruwan masu zanga-zangar adawa da kungiyar Kawance ta NATO/OTAN sun yi ta fafatawa da jami’an tsaro a harabar da Kungiyar ke taro a Chicago inda bayanai ke cewa ana tsare da mutane 45.

Shugabannin kasashen kungiyar sama da 50 ne ke halartan taron inda suke duba tsare-tsare game da kasar Afghanistan, bayan Dakarun kasashen da ke kasar Afghanistan sun cwe zasu janye, a karshen shekara ta 2014.

Mutane da yawa sun yi kwance bisa tituna da ke harabar da ake tarno, inda suke ta ihu cewa basa goyon yadda kasashen su ke kashe makudan kudi a wajen yaki.

Tun a ranar Lahadi aka fara yamutsi lokacin da aka umurci masu zanga-zangan da su kama gabansu daga wannan haraba.

Baya ga mutane 45 da ‘Yan sanda suka ce sun kama, bayanai na nuna cewa akwai ‘Yan sanda Hudu da suka sami raunuka.

Jami’an tsaron kasar Amurka dai sun dauki kwararan matakan tsaro, a Chicago, garin Shugaban Amurka Barack Obama, inda aka gudanar da taron na kwanaki biyu, daya sami halarcin Shugabannin kasashe akalla 50.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.