Isa ga babban shafi
Afghanistan-Amurka

Mutane 11 sun jikkata a zanga-zangar la’antar kona Qur’ani a Afghanistan

An samu mutuwar mutun guda wasu kuma mutane 11 sun jikkata bayan da ‘Yan sanda suka harba harsashe a sama domin tarwatsa masu zanga-zangar la’antar kona Al Quar’ani mai girma da dakarun tsaron NATO suka yi a Afghanistan.

Daruruwan masu zanga-zangar la'antar kona Qur'ani a Afghanistan inda suke harba duwatsu a sansanin dakarun Amurka sai dai wasun su sun samu rauni.
Daruruwan masu zanga-zangar la'antar kona Qur'ani a Afghanistan inda suke harba duwatsu a sansanin dakarun Amurka sai dai wasun su sun samu rauni. REUTERS/Ahmad Masood
Talla

Wani jami’in kiyon Lafiya a kasar ya shaidawa kamfanin Dillacin labaran Faransa AFP cewa mutanen suna fama ne da mikin harsashen da ‘Yan sanda suka harba.

Daruruwan Mutane ne ke ci gaba da gudanar da zanga zanga a birnin Kabul da kudancin birnin Jalalabad a yau Laraba, domin bayyana bacin ransu kan cin zarafin Al Qur’ani da ake zargin sojin kungiyar kawancen Tsaro ta NATO da aikatawa.

Rahotanni sun ce ana kona tayoyin mota a unguwar Hod Khalil, da ke Jalalabad, kusa da sansanin sojin Amurka, yayin da masu zanga-zangar ke Allah waddai da Tsohon shugaban Amurka, George Bush da shugaba Barack Obama mai ci.

A jiya Talata ne Zanga-zanga ta barke a sansanin dakarun Amurka a Bagram bayan samun labarin sun kona Al Quarani mai Girma.

Tuni dai kwamandan Amurka a Afghanistan John Allen ya nemi gafarar abun da ya faru tare da bayar da umurnin kaddamar da bincike akan faruwar al’amarin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.