Isa ga babban shafi
Afghanistan

Zanga-zanga ta barke a Afghanistan bayan kona Al-Qur’ani

Wata sabuwar zanga-zanga ta barke a kasar Afghanistan inda ‘Yan kasar suka fito domin nuna bacin ransu ga rehotanni da ke danganta dakarun tsaron NATO sun kona Al Qur’ani mai girma a kasar.Daruruwan mutane ne suka kewaye sansanin dakarun Amurka a arewacin Kabul tare da gargadin kisa ga Amurkawan.

Wani Dan Afghanistan yana yayata munanan kalamai ga Amurka a dai dai sansanin dakarun Tsaron NATO a Bagrem
Wani Dan Afghanistan yana yayata munanan kalamai ga Amurka a dai dai sansanin dakarun Tsaron NATO a Bagrem REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Kwamandan dakarun Sojin Amurka Janar John Allen ya nemi gafara tare da bada umurnin gudanar da bincike game da rehoton kona Al’Qur’anin da Amurkawan suka yi.

Wani Jami’in dan sanda yace sama da mutane 200 ne suka fito domin gudanar da zanga-zanga a Bagrem.

Kakakin ‘Yandan Sandan yankin Pul-e-charkhi ya shaidawa wakilin Kamfanin Dillacin Labaran Faransa AFP cewa mutane sama da 500 ne suke gudanar da zanga-zanga a sansanin dakarun NATO a saman Titin Jalalabad.

A watan Afrilun bara mutane 10 suka mutu, wasu da dama suka ji rauni bayan gudanar da zanga-zanga a lokacin da wani Ba’amurke Terry Jones ya kona Al Kur’ani.

A watan Jiya wani hoton Bidiyo ya nuna wasu dakarun Amurka suna fitsari saman gawawwakin wasu da ake tunanin ‘Yan kungiyar Taliban ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.