Isa ga babban shafi
Libya-NATO-HRW

NATO ta kashe fararen hula 72 a Libya, inji HRW

A wani Rahoton da Hukumar kare hakkin Dan adam ta Human Rights Watch ta fitar, rahoton yace a bara wani hari da kungiyar NATO ta kai ta sama ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 72 a Libya, tare da zargin kawance kasashen Turai da suka kaddamar da yakin kawar da Gaddafi.

Talla

Rahoton wanda hukumar ta gudanar da bincike akai, hukumar ta Zargi kungiyar NATO da kashe mata 20 da yara 24. Hukumar ta nemi a biya diyyar fararen hular da aka kashe tare da kiran gudanar da binciken hare haren da NATO ta kai ba bisa ka’ida ba.

Fred Abrahams babban Jami’in hukumar mai bayar da shawara yace sansanin dakarun Soji ne NATO ya dace ta kai hari bag a fararen hula ba.

Tun bayan kisan Gaddafi kungiyar NATO ta bayyana samun nasarar yakinta a Libya bayan kai hare hare 26,000 kafin kawo karshen yakin Libya a ranar 31 ga watan Octoba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.