Sauraren karar Kwamandan Serbia, Ratko Mladic a gaban kotu
Tsohon kwamandan Serbia, Janar Ratko Mladic, ya gurfana a gaban kotun Duniya a birnin Hague domin fuskantar zargi 11 na laifukan yaki da kisan kare dangi da keta hakkin bil’adama a yakin Bosnia a shekarar 1992-95.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Janar Mladic shi ne babban jami’I na karshe a yakin Balkan da zai gurfana a gaban kotun Duniya, saboda zargin kashe Musulmi yara maza da Manya sama da 7,000 a Srebrenica.
Sai dai Mladic wanda aka cafke a watan Mayun bara bayan kwashe shekaru 16 ana farautar shi, ya musanta zarge zargen da ake ma shi.
A cewar Mladic duniya ta san ko shi wanene a lokacin da aka fara sauraren karar shi a bara.
“ suna na Janar Ratko Mladic, ina kare mutane na da kasa ta, kuma yanzu zan kare kai na”, inji Mladic.
Wani hoton Bidiyo ya nuna Mladic cikin gungun Musulmi da suka kama a gidan yari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu