Mai gabatar da kara ya nemi a yanke wa Taylor hukuncin shekaru 80 a gidan yari
Babban mai gabatar da kara a shari’ar Charles Taylor tsohon shugaban kasar Liberia, ya nemi a daure tsohon shugaban shekaru 80 a gidan yari bayan kama shi da laifin aikata laifukan yaki a Saliyo.
Wallafawa ranar:
Wasu takardun da suka fito daga ofishin mai gabatar da karan, sun ce wannan hukuncin ya dace da Mista, Taylor, saboda bayar da makamai da taimakawa ‘Yan tawayen da suka hallaka, da nakasa dubu dubatar mutane a kasar Saliyo, mai makwabta da Liberia.
A makon da ya gabata kotun ta hukunta manyan laifuka, ta sami Taylor mai sheakru 64, da laifin taimakawa, wajen aikata laifukan yaki a kasar ta Saliyo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu