Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Obama ya kawo karshen yakin Iraqi

Shugaban Kasar Amurka, Barrack Obama, ya yabawa dakarun kasar, bisa rawar da suka taka, wajen kawo karshen abinda ya kira mulkin kama karya a kasar Iraqi bayan kwashe shekaru Tara ana yaki.

Shugaban Amurka Barack Obama Lokacin da yake jawabi a gaban Daruruwan dakarun kasar bayan kawo karshen yaki Iraki
Shugaban Amurka Barack Obama Lokacin da yake jawabi a gaban Daruruwan dakarun kasar bayan kawo karshen yaki Iraki REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A ranar 31 ga watan Disemba ne Amurka ta ayyana ficewa da sauran dakarunta da suka rage a cikin kasar Iraqi.

A lokacin da shugaban ke jawabi a Arewacin Carolina a gaban daruruwan dakarun kasar, Obama ya yi lale marhabin da su tare da nuna farin cikinsa da tarihin da suka kafa wa Amurka.

Dakarun Amurka kusan 4,500 aka kashe, akalla mutanen Iraqi 60,000 suka mutu a yakin kasar, amma Obama yace Amurka ta kashe kudi sama da dala Trilion daya.

Kawo karshen yakin Iraqi shi ya taimakawa Obama lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2008 inda Amurka ta mayar da hankali a Afghanistan da kuma rikicin cikin gida na rashin aikin yi da ke addabar kasar.

Masu adawa da Obama sun kalubalanci matakinsa na kawo karshen yakin Iraqi domin taimaka masa a yakin neman zabensa, inda suka yi gargadin ficewa daga Iraqi wata hanya ce ta bude kofa ga makwabciyarta Iran.

A wata wasika da Mitt Romney, ya aikawa Obama babban mai adawa da shi a jam’iyyar Republican, yace karrama dakarun abun kunya ne domin mutane da dama na fama da matsalar aikin yi.

A makon nan dakarun Amurka kimanin 5,500 ne suka fice daga Iraqi, kasa da dakaru 170,000 tun fara yakin Amurka a cikin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.