Isa ga babban shafi
Iraki-Amurka

Iraqi ta yi kiran Amurka zuba jari a cikin kasar

Fira Ministan Iraki Nouri al-Maliki ya yi kiran gwamnatin Amurka da ‘yan kasuwarta domin zuba jari a cikin kasar don taimakawa kasar farfado da tattalin arzikinta bayan kwashe shekaru ana yaki a cikin kasar.

birnin Washington lokacin da Obama na Amurka ke ganawa da Maliki Fira Ministan kasar Iraki
birnin Washington lokacin da Obama na Amurka ke ganawa da Maliki Fira Ministan kasar Iraki REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Wannan kiran na shugaban na zuwa a dai dai lokacin da dakarun Amurka ke shirn ficewa Iraki.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a ziyararsa Amurka, Fira Ministan, yace sha’anin tsaro ya inganta kuma yanzu suna neman hanyoyin da zasu inganta al’amurra a Iraki a nan gaba.

Mista Maliki ya kai ziyarar ne birnin Washington domin kulla huldar kasuwanci tsakanin shi manyan attajiran kasarsa .

Bayan ganawarsa da shugaban Amurka Barack Obama, Fira Ministan yace yana fatar ganin tattalin arzikin Iraki ya inganta fiye da kasashen Indiya da China.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.