Isa ga babban shafi
Sri Lanka-UN

Masu zanga zanga sun mamaye ofishin Majalisar Dinkin Duniya

MASU zanga zanga a kasar Sri Lanka, sun sake yiwa ofishin Majalisar Dinkin Duniya tsinke, inda suke bayyana matsayin su, na adawa da shirin gudanar da bincike da Majalisar ke shirin yi, kan cin zarafin Bil Adama.Ministan samar da gidajen kasar, Wimal Weerawansa, wanda ke jagorancin zanga zangar, yace zasu cigaba har sai Majalisar ta janye binciken.Ana zargin Gwamnatin kasar, da anfani da karfin da ya wuce kima, wajen murkushe Yan tawayen Tamil Tigers.Jiya dai da kyar aka fitar da ma’aikatan dake ofishin Majalisar, amma yau da dama daga cikinsu baus samu damar zuwa wurin aiki ba. 

zanga zanga a kasar Sri Lanka
zanga zanga a kasar Sri Lanka
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.