Isa ga babban shafi
Amnesty International

Kungiyar kare hakkin Dan Adam ta zargi yadda Gwamnotoci ke kare masu laifufuka

KUNGIYAR Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International, ta zargi wasu Gwamnatocin kasashen duniya, da zagon kasa wajen hana kotuna hukunta Yan siyasa da suka aikata laifufuka.Rahotan da kungiyar ta fitar yau, ya baiyana cin zarafin jama’a a kasashe 111, da kuma laifufukan yaki a kasar Sri Lanka.Kungiyar ta zargi Amurka da kasashen Turai, da kare Israela, daga fuskantar shari’a kan yakin da ta kaddamar a Gaza.Kungiyar ta kuma zargi kungiyar kasashen Africa ta AU da rashin goyan bayan hukunta shugaban kasar Sudan, Umar Hassan al Bashir, da kuma Majalisar Dinkin Duniya kan rashin daukar matakin da ya dace.Kungiyar ta kuma yaba da hukunta Tsohon shugaban kasar Peru, Alberto Fujimore, saboda laifin cin zarafin jama’a, da kuma Tsohon shugaban kasar Argentina, Reynaldo Bignone, wanda aka samu da laifin sacewa da azabtar da jama’a. 

Amnesty International
Amnesty International
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.