Isa ga babban shafi
Faransa-Belgium

Najim Laachraoui na daga cikin dogaren Isil a Syria

Masu bicinke a kasar faransa sun gano cewa daya daga cikin mutanen dake tsare yanzu haka na da hannu a garkuwar da aka yiwa wasu faransawa a Syria a shekara ta 2013.Mutumin mai suna Najim Laachraoui ya kasance dan aike na musaman na kungiyar ta Isil kamar dai yadda bicinke ya tabbatar. 

Najim Laachraoui mutumin da masu bicinke suka gano cewa ya na daga cikin maharan Faransa
Najim Laachraoui mutumin da masu bicinke suka gano cewa ya na daga cikin maharan Faransa ©AFP/
Talla

Najim Laachraoui dan kasar Belgium kuma daya daga cikin maharan tashar sauka dama tashin jiragen saman Bruxos na ranar 22 ga watan maris shekarar bana ya kasance daya daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da wasu faransawa da yan kungiyar Isil suka yi awon gaba da su a Syria daga shekara ta 2013 zuwa 2014.

Mutanen da yan kungiyar Isil suka yi garkuwa sun hada da Didier francois, Pierre Torres, Edouard Elias da Nicolas Henin dukan su yan jarida da kuma suka tabbatar da cewa mutumin da ya kwashe lokaci ya na mai kula da su an ba shi sunan Abou Idriss ,wanda masu bicinke suka halakanta da Najim Laachraoui.

'Yan kungiyar ta Isil sun salami mutanen a watan afrilu shekarar 2014 bayan da suka kwashe watanni goma a hannu kungiyar a Syria.

Masu bicinke sun gano shi a ranar 9 ga watan satumba shekarar 2015 watanni biyu kafin harin birnin Paris na watan novemba shekarar da ta shude, harin dai na Paris yayi sanadiyar mutuwar mutane 130.

A karshe bicinke ya gano cewa Najim ya kasance wani dan aike na musaman da kuma aka shirya harin birnin Paris da shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.