Mutumin da Ake Zargi Da Hannu a Harin Bam Na Belgium ya ce Sun So Sake Kai Wani Hari A Faransa
Mutumin da ake zargi da hannu wajen harin ta'addanci na Paris, Mohammed Abrini dake hannu, ya bayyana cewa shakka babu shine cikin wani hoton bidiyo da aka gani yana tura keken daukan kaya, a filin jiragen sama na Brussels jim kadan kafin tashin bam na kwanan baya
Wallafawa ranar:
Majiyoyin tsaro na cewa amsa cewa shine zai taimakawa jami'an tsaro a Faransa da kuma Belgium a binciken da suke yi gameda harin ta'addanci a kasashen.
Masu shigar da kara sun fadi yau Lahadi cewa Mohammed Abrini wanda tuni ya amsa hannu a harin kai bam a Paris an gurfanar dashi gaban kotu saboda hannu a harin bam na Brussels.
Wata sanarwa yau a Brussels na cewa Kotu ta umarci a ci gaba da tsare Mohammed Abrini.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu