Isa ga babban shafi
Tunisiya

An kaddamar da Majalisar Shata Kundin Tsarin Mulkin Tunisiya

Kasar Tunisiya ta shiga wani sabon babi a tarihin ta, domin yau Talata aka kaddamar da sabuwar majalisar shata sabon kundin tsarin mulkin kasar, dake zuwa watanni 10 bayan mummunar zanga-zangar data kifar da Gwamnatin kama-karya Zine al-Abidine Ben Ali.

Zaben kasar Tunisiya
Zaben kasar Tunisiya REUTERS/Louafi Larbi
Talla

Manyan Jam’iyyun siyasar kasar ta Tunisiya, sun yi nasarar raba manyan mukaman kasar, sakamakon nasarar zaben da suka samu.

A karkashin wanna yarjejeniya, Hamadi Jebali na Jam’iyar Ennahda, zai rike mukamin Prime Minista, Moncef Marzouki na Congress for the Republic zai rike mukamin shugaban kasa, yayin da Mustafa Ben Jaafar na Jam’iyar Ettakol zai jagoranci Majalisar da aka kaddamar wa yau.

Kamar yadda Ahmed Mestiri, wani jigo wajen gwagwarmayar samun ‘yancin kasar daga FR a shekara ta 1956, bikin kaddamar da sabuwar majalisar ya kasance tamkar ana bikin sake samun 'yancin kasar ce.

Ahmed Mestiri dan shekaru 86 da haihuwa, ya ce yana ganin yanzu ne ma ake kafa Gwamnati a kasar.

Cikin watan 12 na bara nedai sakamakon matsanancin halin rayuwa, jama'a suka nuna fushinsu, inda suka kawar da Gwamnatin Shugaba Zine el-Abidine Ben Ali wanda ya kwashe shekaru 23 yana jan ragamar mulkin kasar.

Wancan zanga-zanga da aka fara a kasar Tunisiia, ita ta yi rassa akasashen Larabawa, musamman inda Shugabannin suka nace su kawai zasu rike kasar ta kowani hali.

Sabuwar majalisar kasar Tunisiya ta na da wakilai 217 wadanda zasu tsara kundin tsarin mulki, da tsara shugabanni nada rinjayen ‘yan Ennahda, wadda kungiyar ‘yan uwa musulmi ke da ita.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.