Isa ga babban shafi
Tunisia

Yau ne ranar karshen yakin neman zabe a Tunisiya

A yau Juma’a ne ake kawo karshen yakin neman zabe a Tunisiya kwanaki biyu a gudanar da zaben farko na ‘Yan Majalisu tun bayan hambarar da Zine El Abidina.Sama da mutane Miliyan bakwai ne ake sa ran zasu kada kuri’a a zaben wanda zai kasance zakaran-gwajin-dafin shewar girka demokradiyya a zanga-zangar adawa da gwamnatocin kasashen Larabawa.Zaben ‘yan Majalisun zai hada da jam’iyyun siyasa da dama, kuma wani bincike ya nuna cewa jam’iyyar musulunci ta Ennahda ce zata samu yawan kuri’u.Sabon tsarin zaben ya bada damar jam’iyyu da dama shiga zaben domin sake fasalta kundin tsarin mulkin kasar.Fira Ministan kasar Beji Caid Essebsi ya yi kiran al’ummar Tunisia su fito kwansu da kwarkwata ba tare da wata fargaba ba domin kada kuri’arsu. 

Katin shaidar zabe a Tunisia
Katin shaidar zabe a Tunisia RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.