Isa ga babban shafi
UN-Libya

Majalisar Dunkin Duniya zata gana da ‘yan tawayen Libya a Tunisiya

Manzo na musamman daga Majalisar Dunkin Duniya, yanzu haka ya isa Tunisiya a wata tattaunawa da ‘Yan tawayen kasar da kuma wakilan gwamnatin Muammar Gaddafi.A cewar Kamfanin Dillacin labaran AFP, tsohon Ministan harakokin wajen kasar Jordan Abdul ilah al-Khatib yace za’a gudanar da taron tattaunawar ne a wata Otel a Tunisiya.Tuni dai Sakataren Majalisar Dukin Duniya Ban Ki-moon ya bayyana imaninsa cewa amfani da karfin Soji ba shi zai kawo karshen rikicin kasar Libya ba.Ban Ki-moon ya yi kira ga Gaddafi da ‘Yan Tawaye da su gaggauta sasanta kansu tare da fito da hanyoyin da za’a kawo karshen zubar da jinin da ake yi a cikin kasar. 

wani dan tawayen Libya a wani hotonsa can birnin Bir al-Ghanam a yammacin Libya,
wani dan tawayen Libya a wani hotonsa can birnin Bir al-Ghanam a yammacin Libya, REUTERS/Bob Strong
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.