Jam’iyyar Musulunci ke kan gaba a zaben Tunisiya
Jam’iyyar musulunci ta Ennahda ta yi ikirarin lashe zaben farko na ‘yan majalisu da aka gudanar tun bayan hambarar da gwamnatin Zine Al Abidine Ben Ali.A yau ne ake sa ran bayyana sakamakon zaben amma Jam’iyyar Ennahda ta bayyana samun nasarar zaben bisa bayanan da ta tattara a runfunan zabe.Yanzu haka kuma magoya bayan Jam’iyyar sun barke da kabbara tare da rera taken Tunisia bayan da shugaban yakin neman zaben jam’iyyar Abdulhamid Jlazzi ya bayyana jam’iyyar Ennahda ce akan gaba.An samu fitowar masu kada kuri’a da kusan kashi 90 domin zaben ‘yan majalisun da zasu sake fasalta kundin tsarin mulkin kasar da zai bada damar zaben sabuwar gwamnati a shekarar 2013
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: