Isa ga babban shafi
Tunisia

An fara kidayar kuri’u a Tunisiya

Shugaban Hukumar zaben kasar Tunisiya, yace gobe talata ne ake saran bada kammalallen sakamakon zaben ‘Yan Majalisun da aka gudanar a karshen mako, wanda ya samu fitar mutane kada kuri’a sama da kashi 90.Kasashen duniya sun yaba da yadda zaben ya gudana, inda ake saran bayyana ‘Yan Majalisu 217 da zasu rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar.Kasar Tunisia ce ta farko ta fara zanga zangar da ta tilastawa shugaba Zine al Abidine Ben Ali sauka daga karagar mulki kafin kasashen Masar da Syria da Libya da sauran kasashen Larabawa suka dauka. 

Wata mata a Tunisia tana kada kuri'arta a zaben 'yan majalisu da aka gudanar
Wata mata a Tunisia tana kada kuri'arta a zaben 'yan majalisu da aka gudanar RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.