Ya zama wajibi Mali ta samar da mafita da shirya zabe- Kungiyar Tarayyar Afirka
Kungiyar Tarayyar Afirka a jiya Asabar ta bukaci kasar Mali da ta samar da mafita na dawo da kuma shirya mika mulki ga farraren fula ta hanyar shirya zabe.Kungiyar ta na mai cewa ana bukatar daukar matakin ne domin mayar da kasar kan tafarkin dimokuradiyya.
Wallafawa ranar:
A farkon makon nan ne dai gwamnatin mulkin sojan kasar ta Mali ta bayar da umarnin dakatar da duk wasu harkokin siyasa, bisa la'akari da bukatar tabbatar da zaman lafiyar a fadin kasar ga baki daya.
al'ummar kasar na fatan zama lafiya,wannan ne babban aiki da majalisar sojin kasar ta saka a gaba a cewar Firaministan kasar Mali Choguel Kokalla Maiga a lokacin da ya amsa wasu daga cikin tambayoyin manema labarai ganin ta yada ake shiga muhawara yan lokuta bayan da majalisar sojin kasar ta soke ayyujan jam’iyyun siyasa.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta nuna matukar damuwarta kan matakin, tana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga dawowar mulkin dimokuradiyya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu