Hukumomin sojin Mali sun haramtawa kafafen yada labarai yada labaran jam'iyyun siyasa
Hukumomin sojin Mali masu rike da madafan ikon wannan kasa a yau Alhamis sun haramtawa kafafen yada labarai buga duk wani labari kan ayyukan jam’iyyun siyasa na wannan kasar, kusan kwanaki daya da sanar da dakatar da wadanan jam’iyyu daga ayukan su.
Wallafawa ranar:
A kasar ta Mali,vayan sanar da dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasa, babbar hukumar sadarwa ta kasa wato HAC a wata sanarwa ta ce “tana gayyatar dukkanin kafafen yada labarai kama daga rediyo, talabijin, jaridu da na yanar gizo da su dakatar da watsa shirye-shirye da suka jibanci ayyukan jam’iyyun siyasa na kasar da kungiyoyi masu aiki da su.
Babbar hukumar sadarwa ta kasa HAC ba ta bayar da karin haske ba a kan gidajen watsa labarai da za a iya baiwa damar fitar da irin wadanan labarai har idan hakan ta kasance a gaba.
Wadannan sabbin takunkumi ne kan duk wani furuci na adawa ko rashin amincewa da shugaban majalisar sojin kasar ta Mali ,wanda ya karbi mulki da karfi a watan Agustan 2020 ta hanyar hambarar da shugaban farar hula Ibrahim Boubacar Keïta.
Wannan sabon salon na zuwa ne a dai dai lokacin da sojoji suka gaza a kan alkawarin da suka dauka, sakamakon matsin lamba daga kungiyar ECOWAS na mika wuya ga farar hula kafin ranar 26 ga Maris, 2024.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu