Isa ga babban shafi

Yakin Sudan ya bazu zuwa yankin da ke da yawan 'yan gudun hijira

Wasu jiragen sama marasa matuka sun kai hari jihar al-Gadaref da ke Sudan, lamarin da ake ganin rikicin da ake yi a kasar ya isa yankin da ake da zaman lafiya kuma mutane ke samun damar yi noma, bayaga ‘yan gudun hijira sama da dubu dari biyar da ke cikinsa.

Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da yakin Sudan ya raba da muhallansu.
Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da yakin Sudan ya raba da muhallansu. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Gwamnan jihar da kuma wasu shaidun gani da ido ne suka tabbatar da kai harin na birnin Gadaref wanda shi ne babban birnin jihar al-Gadaref, jihar da ta kasance karkashin ikon sojojin kasar tun bayan barkewar rikici tsakanin sojojin kasar da kuma dakarun RSF a ranar 15 ga watan Afrelun shekarar bara.

Shaidun gani da ido sun ce akalla kuraman jirage biyu ne suka kaiwa wani sansanin sojin kasar da Gadaref hari da safiyar jiya Talata, sannan sun ji karar ababen fashewa da kuma makaman harko makamai masu linzami, sannan an tura da sojoji a baki daya sassan birnin.

Gwamnan jihar Mohamed Abdelrahman Mahgoub ya tabbatar da batun kai harin duk da dai bai bayyana wadanda suka kaishi ba, sannan ya bukaci fararen hular da suka shiga cikin Shirin ko ta kwana, su shirya bai wa yankin kariya.

A yanzu dakarun RSF ke rike da ikon babban birnin Sudan Khartoum da jihohin Gezira da Darfur da kuma Kordofan wadanda suke a yammacin kasar, ya yin da sojojin kasar ke rike da ikon Arewaci da Gabashin da kuma babbar tashar ruwan kasar a tekun Maliya.

Sama da mutane miliyan 8 da dubu dari biyar ne rikicin na Sudan ya tilasta musu barin gidajensu, sannan kungiyoyin bada agaji suka yi gargadin fuskantar barkewar yunwa a kasar da ke zama ta uku wajen yawan fadin kasa a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.