Isa ga babban shafi

MDD ta cigaba da kai agaji Darfur watanni biyu da dakatar ayyukan

Majalisar dinkin duniya ta ce an mayar da aikin kai kayan agaji zuwa yankin Darfur na Sudan bayan dakatarwa na tsahon watanni biyu saboda tsanantar yaki, lamarin da ya jefa fararen hula cikin halin tsananin yunwa.

Yakin da aka shafe shekara guda ana tafkawa a kasar ya sake rura wutar matsalar
Yakin da aka shafe shekara guda ana tafkawa a kasar ya sake rura wutar matsalar REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya ta ce ayarin manyan motoci makare da kayan abinci sun tsallaka cikin Sudan ta iyakar Chadi a karshen watan jiya na Maris, sai dai bata yi bayani kan lokacin da za’a kuma shigar da wasu kayan ba.

Bayanai sun ce ranar Juma’a kadai tan 1,300 na hatsi ne ya isa iyakar Adre da ke dab da Chadi yayin da ya karasa zuwa yankin yamma da kuma tsakiyar Darfur.

Da yake bayani daraktan hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya a Chadi Pierre Honnorat tun a watan Maris ya ce babu makawa dole a shigar da kayan agaji Darfur, saboda karuwar mutanen da yunwa ke galabaitarwa a kowacce rana lamarin da ke kara dorawa Chadi nauyin karbar ‘yan gudun hijira.

Majalisar dinkin duniya ta yi kiyasin cewa yara dubu 222 ka iya mutuwa saboda tsananin yunwa a cikin watanni masu zuwa matukar ba’a shigar da kayan agaji cikin gaggawa ba, inda ta ce akwai bukatar tattara dala biliyan 2.7 don tallafawa fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.