Isa ga babban shafi

RSF ta amince da kiran tsagaita wuta a watan Ramadan

Rundinar tawayen RSF a Sudan ta yi maraba da kiran da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi na dakatar da kai hare-hare a watan Ramadan, wanda hakan zai ba da damar tsagaita wuta a yakin da aka shafe watanni 11 ana gwabzawa.

Shugaban 'yan tawayen RSF Mohamed Hamdan Dagalo da mutanensa.
Shugaban 'yan tawayen RSF Mohamed Hamdan Dagalo da mutanensa. AFP - -
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar, RSF ta bayyana fatan cewa kudurin komitin sulhu zai rage wa al'ummar Sudan wahalhalun da suke fuskanta, ta hanyar tabbatar da isar da kayayyakin jin kai cikin kwanciyar hankali da share fagen siyasa da zai kai ga tsagaita wuta ta dindindin.

 

Jakadan kasar Sudan a Majalisar Dikin Duniya Al-Harith Idriss Al-Harith Mohamed, ya shaida wa majalisar a ranar Alhamis cewa, shugaban kwamitin rikon kwarya na kasar ma, ya yaba da wannan kira da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi na neman tsagaita bude wuta.

A watan Afirilun 2023 ne yaki ya barke a Sudan tsakanin sojojin mulkin rikon kwaryar kasar da rundinar kai agajin gaggawa ta RSF bayan rashin fahimta da suka samu, a daidai lokacin da kasashen duniya ke kira da a mika mulkin kasar hannun fararen hula. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.