Isa ga babban shafi

MDD tayi kakkausar suka akan yadda ake take hakkin bil'adama a yakin Sudan

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da mummunan cin zarafi da ake tafkawa a yakin da ake fafatawa a Sudan tsakanin sojojin kasar da dakarun kai daukin gaggawa na RSF.

Wasu 'yan Sudan a garin Adre, bayan da suka tsere daga yankin Darfur, yayin kokarin tsallaka iyakar kasar tasu zuwa cikin Chadi. 4 ga Agustan, 2023.
Wasu 'yan Sudan a garin Adre, bayan da suka tsere daga yankin Darfur, yayin kokarin tsallaka iyakar kasar tasu zuwa cikin Chadi. 4 ga Agustan, 2023. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Tun a watan Afrilun shekarar da ta gabata wani kazamin fada tsakanin Hafsan Sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, kwamandan rundunar RSF.

Fadan ya bazu daga babban birnin kasar Khartoum zuwa kudu maso yammacin Sudan, inda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da raba kusan mutane miliyan takwas da muhallansu, a cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR).

A wannan yakin dai an samu matsalolin gallazawa mata da cin zarafin kananan yara da kuma kisan gilla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.