Isa ga babban shafi

EU ta kakaba wa kamfanoni 6 takunkumai kan rikicin Sudan

Majalisar Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da kudirin kakaba wa wasu kamfanoni 6 takunkumai, saboda hannun da suke da shi a yakin da ake gwabzawa a Sudan.

Wasu 'yan Sudan a garin Adre, bayan da suka tsere daga yankin Darfur, yayin kokarin tsallaka iyakar kasar tasu zuwa cikin Chadi. 4 ga Agustan, 2023.
Wasu 'yan Sudan a garin Adre, bayan da suka tsere daga yankin Darfur, yayin kokarin tsallaka iyakar kasar tasu zuwa cikin Chadi. 4 ga Agustan, 2023. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Matakin majalisar ta EU zai ba da damar kwace kadarorin kamfanonin da kuma dakile ayyukan da suke yi na sama wa sojojin gwamnati da dakarun RSF da suka yi tawaye makamai a yakin Sudan da ya kazanta, bayan barkewarsa a cikin watan Afrilun 2023.

Sai dai yayin zanta wa da sashin Hausa na RFI, Abdulhakeem Garba Funtua masanin siyasar kasa-da-kasa ya ce takunkumai kawai ba za su wadatar ba wajen dakile tasirin rura wutar rikicin kasar ta Sudan.

00:59

AbdulHakeem Garba Funtua kan takunkuman da aka lafta wa wasu kamfanoni sabod rikicin Sudan

A cikin watan Nuwamban shekarar bara, hukumar gudanarwar kungiyar kasashen Turai EU, ta yi gargadin cewa akwai barazanar sake fuskantar wani kisan kare dangin a yankin Darfur na Sudan, inda a rikicin kabilancin da aka gwabza tsakanin shekarar 2003 zuwa 2008, aka kashe mutane dubu 300,000, yayin da wasu sama da miliyan 2 suka rasa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.