Dubban mutane sun tsere daga birnin Wad Madani na Sudan
Dubban mutanne ne suka yi ta arcewa daga birnin Wad Madani na kasar Sudan a jiya Asabar sakamakon wani fada da ya barke tsakanin dakarun kai daukin gaggawa na RSF da rundunar sojin kasar, lamarin da ya bude wani sabon babi a rikicin da suka shafe watanni 8 suna gwabzawa.
Wallafawa ranar:
Hotunan bidiyo sun nuna dimbim mutane, akasari wadanda suka shiga birnin don neman mafaka daga rikicin da ake yi a Khartoum su na kwashe kayansu su na barin birnin a kasa.
Rundunar sojin Sudan wadda ke rike da birnin tun da yakin ya barke a Kharoum sun kaddamar da harin sama kan dakarun RSF a gabashin brnin, a kokarin da suke na tura su baya.
A watan Afrilu ne fada ya barke tsakanin dakarun kai daukin gaggawa na rundunar RSF da sojojin Sudan, lamarin da ya sanadin mutuwar dimbim mutane sakamakon ci gaba da ruruwada wutar rikicin ke yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu