Isa ga babban shafi

An kashe mutum 40 a kan iyakar da ta raba Sudan ta Kudu da Sudan

Kimanin mutane 40 ne wadanda yawancinsu fararen hula ne, aka kashe a wani rikici a yankin da ake takaddama akai da ke kan iyakar Sudan ta Kudu da Sudan, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Manjo Janar Peter Gadet daga hagu kenan, yayin da yake jawabi ga dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Abyei, ranar 2 ga Yuli, 2008.
Manjo Janar Peter Gadet daga hagu kenan, yayin da yake jawabi ga dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Abyei, ranar 2 ga Yuli, 2008. AFP PHOTO/UNMIS/TIM MCKULKA
Talla

An yi ta samun tashe-tashen hankula a yankin Abyei a tsakanin gungun 'yan kabilar Dinka da ke gaba da juna, sakamakon takaddamar da ake yi a kan iyakokin da ake samun haraji mai tsoka sakamakon cinikin kan iyaka.

Yankin Abyei dai yanki ne mai arzikin man fetur da ke karkashin hadin gwiwar Sudan ta Kudu da Sudan, wadanda dukkansu ke da alaka da shi.

Ministan yada labaran yankin, Bulis Koch ya ce, a hare-haren da aka kai a ranakun 2 da 3 ga watan Fabrairu, an kona kasuwanni da dama, tare da kwashe dukiyoyi masu tarin yawa, kuma an kashe fararen hula 19 tare da jikkata wasu 18.

An kuma kashe wasu mutane 18 a wasu hare-haren da aka kai a ranar Lahadi, ciki kuwa har da kananan yara uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.