Isa ga babban shafi

Jagoran mulkin sojin Sudan ya yi watsi da tayin sulhu da dakarun RSF

A wani jawabi da ya gabatar gaban dandazon sojojin Sudan, shugaban mulkin sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan ya bayyana kwarin gwiwar samun galaba kan barazanar mayakan RSF da suka shafe watanni 4 suna gwabza yaki da gwamnati.

Jagoran mulkin Sojin Abdel Fattah al-Burhan daga dama tare da Mohamed Hamdan Daglo jagoran dakarun RSF.
Jagoran mulkin Sojin Abdel Fattah al-Burhan daga dama tare da Mohamed Hamdan Daglo jagoran dakarun RSF. © AP Photo - Montage RFI
Talla

Burhan wanda ya bayyana dakarun kai daukin gaggawar na RSF a matsayin maciya amanar kasa ya ce gwamnati za ta murkushe su ba tare da amsa tayin wasu kasashe na yin sulhu da su ba.

A cewar shugaban, ko kadan ba za su lamunci yin sulhu da maciya amanar kasa ba, wadanda suka zabi jefa jama’ar Sudan cikin bala’i.

Jawabin na al-Burhan yayin ziyarar da yake yi yanzu haka a jihar Port Sudan karon farko tun bayan faro yakin kasar a watan Aprilu da ya kashe dubun dubatar fararen hula, ya ce idan har dukkanin jerin tattaunawar da bangarorin suka shiga da juna bai kai ga nasarar kawo karshen yakin ba, ko shakka babu amfani da karfi ne kawai zai kawo karshen dakarun na RSF.

Dakarun Sojin Sudan a ci gaba da yakin da suke da mayakan RSF.
Dakarun Sojin Sudan a ci gaba da yakin da suke da mayakan RSF. © AFP

Kalaman al-Burhan dai na zuwa ne kwana guda bayan jagoran na RSF ya bude kofar tsagaita wuta tare da tattaunawar sulhu da bangaren gwamnati da ke matsayin karon farko da ya bukaci hakan cikin watanni 4 da faro yakin.

Wasu bayanai sun ce bayan kammala rangadin sansanonin sojin na Sudan da al-Burhan ke yi, kai tsaye zai nufi kasashen Saudiya da Masar don tattaunwa da mahukuntan kasashen biyu wadanda tun farko su ne suka shiga tsakani don shawo kan rikicin kasar.

Dakarun RSF da ke yaki da gwamnatin Sudan.
Dakarun RSF da ke yaki da gwamnatin Sudan. AFP - -

Zuwa yanzu miliyoyin ‘yan Sudan ne ke gudun hijira a kasashen makwabta da suka kunshi Chadi da Sudan ta Kudu da kuma Habasha baya ga Masar, yayin da yunwa ke ci gaba da tsananta, baya ga karuwar cin zarafin mata da kananan yara.

A bangare guda Majalisar Dinkin Duniya ta zargi dukkanin bangarorin biyu da aikata laifukan yaki a rikicin na fiye da watanni 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.