Isa ga babban shafi

Red Cross ta roki kasashen duniya su tausaya wa Sudan

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta yi kira ga kasashen duniya da su kara kaimi wajen samar da kudaden da za a yi amfani da su wajen agaza wa al’umar Sudan da rikici ya dai-daita, a yayin da aka shiga wata na hudu da ake rikici a kasar.

Wasu kananan yara da rikicin Sudan ya shafe su.
Wasu kananan yara da rikicin Sudan ya shafe su. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

A cewar Sakatare Janar na kungiyar Jagan Chapagain, kashi 7 kawai aka iya karba daga cikin dala miliyan 45 da kasashe suka alkawarta samarwa, kuma wannan ya sa ya zuwa yanzu ba a samu damar aiwatar da abin da ya kamata ba kamar yadda aka tsara.

Red Cross ta yi wannan kira ne saboda tsananin wahalar da al’umar kasar suka samu kansu a ciki, domin suna cikin matukar bukata ta tallafin abinci da abin sha da magunguna, sannan a kullum yanayin kara tabarbarewa yake yi, abin da ke jefa su cikin tsananin bukatar dauki cikin gaggawa, wannan ya sa ake shelar ganin kasashen duniya sun bada hadin kai domin ceto al’umar kasar daga ci gaba da kasancewa cikin mawuyacin hali.

Da dama daga cikin al'ummar Sudan sun tsere daga kasar saboda tashin hankali.
Da dama daga cikin al'ummar Sudan sun tsere daga kasar saboda tashin hankali. © AP

A halin da ake ciki, kusan mutane miliyan 3 da rabi ke zaman gudun hijira a wasu sassa na cikin kasar, yayin da sama da miliyan 1 suka ketare iyaka zuwa kasashe da ke makotaka da kasar ta Sudan.

Sudan ta fada cikin rudanin ne a cikin watan Afrilun wannan shekara, lokacin da rikici tsakanin dakarun sojin Abdel Fattah Burhan da mayakan Mohammed Hamdan Daglo, ya barke a birnin Khartoum da wasu sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.