Isa ga babban shafi

An cika kwanaki 100 da barkewar yakin Sudan duk da kokarin kasashe na shiga tsakani

A wannan Lahadi 23 ga watan Yuli aka cika kwanaki 100 da fara yakin Sudan tsakanin sojoji da rundunar RSF, rikicin da yaki ci, yaki cinyewa duk da kokarin da kasashen Afirka da duniya keyi na shawo kan sa. 

Janar-janar din Sudan biyu masu rikici da juna Abdel Fattah al-Burhan Mohamed Hamdan Daglo.
Janar-janar din Sudan biyu masu rikici da juna Abdel Fattah al-Burhan Mohamed Hamdan Daglo. © AP
Talla

Wannan rikici ya barkene a ranar 15 ga watan Afrilun wannan shekara, lokacin da aka fara kokawar iko tsakanin sojojin gwamnati karkashin jagorancin Janar Abdel-Fattah Burhan da kuma bangaren RSF wanda mataimakin sa Mohamed Hamdan Daglo ke jagoranta, abinda yayi sanadiyar raba mutane sama da miliyan 3 da gidajen su, cikin su harda sama da dubu 700 da suka tsere zuwa kasashen dake makotaka da Sudan. 

Kokarin shiga tsakani

Kasar Saudi Arabia da Amurka sun yi iya bakin kokarin su na samar da tsagaita wuta har sau 3, amma bangarorin sun ki yarda su dakatar da yakin na dindindin abinda yayi sanadiyar hallaka mutane 1,136 wadanda hukuma ta tantance. 

Ya zuwa yanzu babu wani bangare daga cikin masu fadan da yayi ikrarin samun nasara, yayin da jama’ar kasar ke ci gaba da shan wahala. 

Kungiyar kasashen dake Gabashin Afirka da kungiyar kasashen Afirka ta AU duk sun yi iya bakin kokarin su na shiga tsakani amma bangarorin biyu sun ki sauraron su. 

A makon jiya kasar Habasha ta shirya wani taro wanda ya kunshi kasashen dake makotaka da Sudan da zummar lalubo hanyar da za’a shawo kan bangarorin amma har ya zuwa wannan lokaci ana ci gaba da kai munanan hare hare a tsakanin bangarorin da basa ga maciji da juna. 

A makon jiya, bangarorin sun sake tura wakilan su domin shiga wata sabuwar tatttaunawa a Jeddah, sai dai rahotanni sun ce har ya zuwa wannan lokaci ba’a fara tattaunawar gaba da gaba ba a tsakanin wakilan, kamar yadda ministan harkokin wajen Sudan ya tabbatar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.