Isa ga babban shafi

Bangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun koma tattaunawar sulhu a Jedda

Wakilan gwamnatin Sudan sun isa birnin Jeddah na kasar Saudiya, don ci gaba da tattaunawa da wakilan sojojin kai daukin gaggawa na RSF da suka kwashe sama da watanni uku suna rikici da juna, kamar yadda wata majiyar gwamnatin kasar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters. 

Janar Al-Burhane yayin ziyararsa ga dakarun kasar da ke yaki da RSF.
Janar Al-Burhane yayin ziyararsa ga dakarun kasar da ke yaki da RSF. AP
Talla

A farkon watan Yunin da ya gabata ne kasashen Saudiya da kuma Amurka suka dakatar da tattaunawar da su ke shiryawa bangarorin biyu, sakamakon yadda suka sabawa yarjejeniyar tsagaita wutar da ta shiga tsakaninsu biyo bayan kaiwa juna farmakin da ya kashe fararen hula. 

Sai dai a ranar Alhamis din da ta gabata, kasar Masar ta fara wata tattaunawa da bangarorin da dukkaninsu suka amince da ita, a kokarin kawo karshen rikicin kasar da Majalisar Dinkin Duniya ke bayyana yiwuwar ya juye zuwa mafi munin yakin basasa. 

A baya an sha cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin amma ba a kai ga nasarar kawo karshen rikicin na kusan watanni 4 da ya yi sanadiyyar rasa rayukan fararen hula fiye da dubu 3 baya fa raba masu kusan miliyan 3 da muhallansu.

Wasu daga cikin ‘yan gudun hijiran Sudan a Libya sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta kai musu dauki, musamman yadda su ke fama da matsalar inda za su zauna da kula da lafiyar wadanda suka samu rauni. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.