Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta bankado tarin laifukan cin zarafin Mata a Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta bankado tarin laifukan cin zarafin mata daga dukkanin bangarorin da su ke yakar juna a Sudan, rahoton da ke zuwa bayan Amurka ta yi zargin muzantawa mata tare da azabtar da su dai dai lokacin da yakin ke ci gaba da tsananta.

Rikicin na Sudan ya jefa tarin Mata a halin kakanikayi.
Rikicin na Sudan ya jefa tarin Mata a halin kakanikayi. © AP - Sam Mednick
Talla

Tawagar jami’an Majalisar yayin jawabinsu gaban kwamitin tsaro sun bayyana cewa galibin matan da suka tsere zuwa jihar Port Sudan sun hadu da mummunan cin zarafi ta hanyar fyade daga sojojin bangarorin da ke yaki da juna.

Edem Wosornu wadda ita ce daraktar shirye-shirye da ayyukan wayar da kai na hukumar jinkan majalisar bayan ziyarar gani da ido da ta kai yankin da rikicin ya fi tsananta a Sudan makwanni 2 da suka gabata, ta ce ta samu damar zantawa da tarin mata wadanda suka fuskanci cin zarafi.

A cewar jami’ar rukunin matan da suka tsinci kansu a wannan matsala sun hada da manya da kananun yara wanda ya tilasta musu tserewa daga matsugunansu.

Ms Wosornu ta ce mata da dama ma’aikata da suka kunshi ma’aikatan asibiti da malaman makaranta sun tsere daga yankunan saboda azabtarwa da cin zarafi baya ga rashin biyan albashi.

Tun a ranar 15 ga watan Aprilu ne yaki ya barke a Sudan tsakanin Sojojin kasar da dakarun kai daukin gaggawa na RSF wanda zuwa yanzu ya raba iyalai kusan miliyan 3.2 da muhallansu ciki har da dubu 900 a makwabta yayinda wasu miliyan 20 ke fama da matsananciyar yunwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.