Isa ga babban shafi

Rikicin Sudan na gab da juyewa zuwa mafi munin yakin basasa a Afrika- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Sudan na gab da fadawa yakin basasar da zai wargaza tsaron ilahirin kasashen yankin, gargadin da ke zuwa bayan harin jiya asabar da ya kashe fararen hula 22.

Janar Abdel-Fattah Burhan tare da dakarun kasar a birnin Khartoum.
Janar Abdel-Fattah Burhan tare da dakarun kasar a birnin Khartoum. © AP
Talla

Ma’aikatar lafiyar Sudan ta tabbatar da mutuwar mutanen 22 a harin wanda jiragen yaki suka yi luguden wuta kan birnin Omdurman na yankin Dar al-Salam mai makwabtaka da Khartoum fadar gwamnatin kasar.

Bayan shafe kusan watanni 3 ana gwabza yakin tsakanin manyan janar din Sojin kasar biyu da ya jefa fararen hula a garari, harin jiragen yakin na jiya na daga cikin hare-hare mafiya tayar da hankali da aka gani a baya-bayan nan.

Dubun dubatar 'yan Sudan ne ke ci gaba da tserewa daga muhallansu a kowacce rana saboda tsanantar rikicin.
Dubun dubatar 'yan Sudan ne ke ci gaba da tserewa daga muhallansu a kowacce rana saboda tsanantar rikicin. © (AP Photo)

Zuwa yanzu mutanen da suka mutu a yakin na Sudan ya kai dubu 3 yayinda wadanda suka tsira ke ci gaba da kokawa game da matsaloli masu alaka da cin zarafi musamman ga mata da ke fuskantar fyade sai kuma hare-haren kabilanci tsakanin kabilun da suka jima suna rikici tsakaninsu.

Majalisar dinkin duniyar ta yi zargin cewa akwai yiwuwar aikata laifukan yaki a yankin Darfur da ya yi kaurin suna wajen rikicin kabilanci.

A cewar Majalisar matukar ba a dauki matakan kawo karshen yakin tsakanin Sojin gwamnati da dakarun RSF ba ko shakka babu matsalar za ta kai inda ba ayi zato ba kuma zata yi illa ga ilahirin yankin ba kadai kasar ta Sudan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.