Isa ga babban shafi

Hare-haren kabilanci sun kashe mutane 52 a iyakar Sudan da Sudan ta kudu

Fiye da mutane 50 suka mutu ciki har da mata da kananan yara a wani sabon rikici da ya barke a yankin Abyei da ke kan iyakar Sudan da Sudan ta kudu, rikicin da ke zuwa bayan hare-haren kungiyoyi masu rike da makamai.

Wani yanki da ya fuskanci hare-haren ta'addanci a Sudan ta kudu.
Wani yanki da ya fuskanci hare-haren ta'addanci a Sudan ta kudu. REUTERS/Joe Penney
Talla

Alkaluman da mahukuntan yankin suka bayar a jiya Litinin sun tabbatar da mutuwar mutane 52 a hare-haren wadanda aka bayyana da mafiya muni da yankin ya gani tun bayan makamantansu a shekarar 2021.

Rikicin yankin na Abyei mai alaka da takaddama kan bangaren da ke da mallakin yankin tsakanin Sudan da Sudan ta kudu, ministan yada labarai na yankin Bulis Koch ya ce baya ga mutanen 52 da suka mutu a hare-haren akwai kuma wasu 64 da suka jikkata.

Yankin na Abyei mai arzikin man fetur, yanzu haka na fuskantar jagoranci daga bangarorin Sudan da Sudan  ta kudu, yayinda bangarorin kungiyoyin da ke rike da makamai daga kasashen biyu ke ci gaba da yakar juna, wanda a lokuta da dama sukan kaddamar da hare-haren da ka kai ga asarar dimbin rayuka.

Tuni mahukuntan yankin na Abyei suka sanar da sanya dokar hana fita a kokarin shawo kan rikicin, wanda ya kai ga kisan jami’in wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dan kasar Ghana.

Zuwa yanzu akwai tarin fararen hular da rikicin ya tilastawa barin matsugunansu,  wadanda ke ci gaba da samun matsugunan wucin gadi a sansanin Majalisar Dinkin Duniya.

Ko a cikin watan Nuwamban bara, sai da makamancin rikicin a yankin na Abyei ya hallaka mutane 32.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.