Isa ga babban shafi

Kimanin mutane miliyan 5 ne za su fuskanci yunwa a Sudan - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a cikin watanni masu zuwa, kimanin mutane miliyan biyar ne za su fuskanci matsananciyar yunwa a Sudan.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a cikin watanni masu zuwa, kimanin mutane miliyan biyar ne za su fuskanci matsananciyar yunwa a Sudan.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce a cikin watanni masu zuwa, kimanin mutane miliyan biyar ne za su fuskanci matsananciyar yunwa a Sudan. REUTERS - EL TAYEB SIDDIG
Talla

Jami’in kula da ayyukan bada agaji na Majalisar Martin Griffiths ne ya yi gargadin hakan, inda ya ce akwai bukatar Kwamitin Tsaro na Majalisar ya dauki matakan da suka kamata.

Griffiths ya ce, matsalar ta yunwan ta faruwa ne sakamakon mummunan tasirin da rikicin kasar ya haifar wa bangaren noma, da lalata manyan ababen more rayuwa da rayuwa da aka yi wanda ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci da hauhawar farashin kayayyaki, da cikas ga ayyukan jin kai, da kuma karncin matsugunan da mutane ke fuskanta.

Ya ce akwai yuwuwar wasu daga cikin mutanen da ke zaune a Yammaci da kuma Tsakiyar Darfur, za su fuskanci matsalar ta yunwa sakamakon yadda lamuran tsaro ke kara tabarbarewa.

Jami’in ya ce akwai kimanin yara dubu dari 730 a fadin kasar ta Sudan da za su fuskanci matsanancin matsalar karancin abinci mai gina jiki, ciki kuwa har da yara dubu dari 240 da ke yankin Darfur.

Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da yakin Sudan ya raba da muhallansu.
Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da yakin Sudan ya raba da muhallansu. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA

Tun bayan barkewar yaki tsakanin dakarun sojin kasar da kuma na rundunar kai daukin gaggawa RSF a ranar 15 ga watan Afrelun bara, Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane miliyan 25 kwatan-kwacin rabin yawan mutanen kasar ne ke bukatar agaji bayaga mutane kusan miliyan 8 ta suka tsallaka kasashe makwafta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.