Isa ga babban shafi

Najeriya ta ayyana wasu mutane 9 da cibiyoyi 6 a matsayin masu daukar nauyin ta'addanci

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana sunan Tukur Mamu da karin wasu mutane 14 a matsayin masu daukar nauyin ta’addanci a kasar.

Tukur Mamu
Tukur Mamu © Vanguard
Talla

Mamu na tsare a hannun Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS tun watan Satumban 2022.

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata doguwar takarda da hukumar da ke tattara bayanan sirri kan shige da ficen kudade ta fitar, inda ta ce, cikin mutanen akwai guda 9 da ke da alaka da kasuwanci da kuma 6 da ke hada-hadar sauyin kudade.

Hukumar ta ce a wani taro da ta gudanar da yammacin jiya ta bada jerin sunayen mutanen tare da bada shawarar gudanar da bincike a kansu.

NFIU ta ce Mamu ya taka rawa wajen samar wa da ‘yan ta’addda kudade ta hanyar karba da kuma kai musu kudaden fansa na adadin kudi dala dubu 200 da ke da alaka da mutanen da kungiyar ISWAP ta sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Harin jirgin kasa kan hanyar Abuja-Kaduna
Harin jirgin kasa kan hanyar Abuja-Kaduna © AP

Daga cikin sauran mutanen, akwai wani mutum da ya kulla tare da samar da kudaden da aka yi amfani da su wajen kai harin ta’addancin da ya faru a Cocin St.Francis Catholic da ke Owo a jihar Ondo da kuma harin da aka kai gidan gyaran hali da tarbiyya na Kuje da ya faru ranar 5 ga watan Yulin 2022.

Cocin Owo ranar da aka kai kari
Cocin Owo ranar da aka kai kari REUTERS - TEMILADE ADELAJA

Akwai kuma wani mutum na daban da hukumar ta ce yana da alaka ta kud-da-kud da kungiyar ta’addanci ta Ansarul Muslimina Fi Biladissudan da ke da alaka da kungiyar Al-Qaeeda wadda ke aikinta a yankin arewacin Afrika.

Bincike ya nuna cewa mutumin ya sami horo na musamman kan harkokin kudi da ta’adddanci karkashin wani mutum mai suna Muktar Belmokhtar, wanda aka fi sani da “Mai ido daya” shugaban kungiyar Al-Murabtoun Katibat ta AQIM da ke gudanar da ayyukan ta’addanci a kasashen Algeria da Mali.

NFIU ta kuma ce wannan mutum dai shi ne mai tsaron lafiyar jagoran kungiyar Boko Haram tsagin Ansaru, Mohammed Usman wanda aka fi sani Khalid Al-Bamawi.

Hukumar ta ce wadannan mutane sun kware wajen tsarawa da kuma samar da kudaden da za a yi amfani da su wajen kai hari, da kuma shiga tsakanin kungiyoyin ta’addanci da masu taimaka musu wajen kera makamai musamman bama-bamai.

Kazalika akwai wani mutum da ke da alaka ta kai-tsaye kan harkokin kudade da kungiyar IS ta yammacin Afrika da ke Okene.

Hukumar ta ce mutanen sun fara alaka ta kai-tsaye da kungiyar Boko Haram a 2012, inda kuma daga baya suka zama masu shiga tsakani wajen kulla yadda za a kai hare-hare ko kuma samar da kudade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.