Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun yi garkuwa da almajirai a jihar Sokoto

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautta zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wasu daliban wata makarantar allo da ba a tantance adadinsu ba a garin Gidan Bakuso da ke karamar hukumar Gada ta jihar Sokoto.

Hoto don misali.
Hoto don misali. © dailypost
Talla

Rahotanni na cewa an sace daliban ne datsakan daren jiya Jumma'a.

Shugaban makarantar, Malam Liman Abubakar, ya shaida wa manema labarai cewa kawo yanzu ba a ji duriyar dalibai 15 ba, amma suna ci gaba da binciken daliban da ba a gani ba.

A cewar Malamin, ‘yan  bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe dayan daren jiya, inda suka harbe mutum daya sannan suka yi awon gaba da wata mata.

Abubakar ya kara da cewa, ba wannan ne karon farko da ‘yan bindiga suka kai hari kauyen ba.

Jihar Sokoto na daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.