Isa ga babban shafi

Najeriya: An kashe 'yan bindiga da dama a harin daukar fansa da suka kai Sokoto

Rahotanni daga Najeriya na cewa ‘yan bindiga da dama ne aka kashe a  yayin wani harin daukar fansa da suka kai kauyen Tukandu da ke mazabar Sakkwai ta karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin kasar.

Misalin 'yan bingida.
Misalin 'yan bingida. Jakarta Globe
Talla

‘Yan bindigar sun gamu da ajalinsu ne da misalin karfe 2  na ranar Talata a lokacin da suka kai samame kauyen da zummar daukar fansa a kan kashe wani abokinsu da aka yi a ranar Litinin.

An ruwaito cewa ‘yan bindigar sun yi yunkurin kai wa kauyen farmaki ne a ranar Litinin, amma suka gamu da turjiya daga mazauna kauyen, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu ciki har da wani dan bindiga.

Ganin cewa ‘yan bindigar za su kawo harin daukar fansa ya sa al’ummar suka bar kauyen, inda suka bar sojojin da aka jibge don samar da tsaro.

‘Yan bindigar, wadanda ba su san da shirin da aka yi ba, sun kutsa kauyen da misalin karfe 10 na safe, kuma suka gamu da wuta daga sojojin da ke kauyen, inda fada ya barke  na tsawon sa’o’i.

Wani mazaunin kauyen, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce an kashe ‘yan bindiga da dama a gwabzawar da aka yi, a yayin da wasu dakarun kasar suka samu raunuka na harbin bindiga.

Ya  kara da cewa an kwace bubura 12 da bindigogi kirar  AK 47 guda 3 daga hannun ‘yan bindigar.

Mai bada shawara ga gwamnan jihar Sokoto a fannin tsaro, Kanar  Ahmed Usman ya tabbatar da aukuwar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.